Bayern Munich ta lashe kofin Jamus

Bayern
Image caption 'Yan wasan Bayern Munich na murnar lashe kofin Jamus

Bayern Munich na kan hanyar lashe kofina uku a bana bayan ta daga kofin German Cup inda ta lallasa Werder Bremen daci hudu da nema a wasan karshe.

Arjen Robben ne ya zira kwallon farko kafin Ivica Olic da Franck Ribery da Bastian Schweinsteiger duk suma suka zira dai dai.

Dama dai Bayern Munich ta riga ta lashe gasar Bundesliga ta Jamus na bana.

Wannan ne karo na 15 da Beyern Munich ta lashe wannan kofin sannan kuma karo na takwas data lashe kofina biyu a Jamus a shekara guda.

Bayern dai zata kara da Inter Milan a wasan karshe na gasar zakarun Turai wato Champions League a ranar 22 ga watan Mayu a filin Real Madrid wato Bernabeu Stadium.