Atletico Madrid ta lashe gasar Europa

atleticomadrid
Image caption Kwallon da Diego Forlan ya zira wacce ta dakile fatan Fulham na lashe gasar

Atletico Madrid ta doke Fulham da ce 2-1 a wasan karshe na gasar cin kofin Europa da aka gudanar a filin wasa na Nordbank Arena da ke Hamburg.

Tsohon dan wasan Manchester United Diego Forlan ya raba gaddama tsakanin kungiyoyin biyu, bayanda ya zira kwallo a mintunan karshe na wasan.

Bayan an shafe minti 90 ana fafatawa sakamako yana daya da daya sai aka tafi karin lokaci na minti talatin kuma a dai dai minti na 116 ne Diego Forlan ya zira kwallon da ta basu damar lashe gasar.

Kociyan Atletico Madrid Quique Sanchez Flores, ya bayyana farin cikin sa, yana mai cewa wannan ba karamin tarihi ba kungiyar ta kafa.

Shi ko Diego Forlan cewa yayi sun cancanci su lashe gasar, domin dama suna da kwarin gwiwar yin hakan.

Kafin dai Fulham ta zo wannan mataki, sai da ta doke kungiyoyi irinsu Juventus da Hamburg. Yayinda ana ta bangaren Atletico Madrid, ta doke kungiyoyi irinsu Liverpool.