Gebrselassie ya lashe tseren Manchester

Dan kasar Habasha Haile Gebrselassie ya lashe tseren fanfalakin Manchester a karo na uku a ranar lahadi.

Dan shekaru talatin da bakwai da haihuwa, Gebrselassie ya taba samun kyautar zinare har sau biyu a gasar Olympics sannan kuma ya lashe tseren sau hudu na duniya.

Dan kasar Spaniya Ayad Lamdessem shine ya zamo na biyu a tseren na Manchester na kilomita goma sannan dan Ukraine Sergiy Lebid ya zamo na uku.

Werknesh Kidane ne ta lashe tseren mata a Manchester din.