Inter Milan ta lashe gasar serie A

Etoo
Image caption Dan Kamaru Samuel Etoo ya haskaka a bana a gasar serie A

Inter Milan na kan hanyar ta na lashe gasa uku a bana, bayan ta lashe gasar serie A ta Italiya a karo na biyar a jere a ranar karshe na kakar wasan Italiya.

Kungiyar karkashin jagorancin Jose Mourinho ta lashe gasar ce bayan ta doke Siena daci daya me ban haushi inda Diego Milito ya zira kwallon.

Ita kuwa As Roma ta karke ta biyu ne bayan ta lallasa Chievo daci biyu da nema.

A farko watannan ne Inter ta doke Roma a gasar cin kofin Italiya sannan kuma zata kara da Bayern Munich a wasan karshe na gasar zakarun Turai.