Lord Triesman zai ajiye mukaminshi

Lord Treisman
Image caption Kalaman Lord Treisman zasu iya kawowa Ingila cikas

Shugaban kwamitin yinkurin Ingila na daukar bakuncin gasar cin kofin duniya a shekara 2018 Lord Triesman zai ajiye mukaminshi bayan rahotanni sun nuna cewar yana mummunar sukar abokan takara.

Lord Triesman ana zarginshi cewar yayi wasu kalamai marasa dadi akan jami'an kasar Rasha dana Spaniya akan batun gasar cin kofin duniya don su hada bakinsu, Spaniya ta taimakawa Rasha a yinkurin Rashar na daukar bakuncin gasar a shekara ta 2018.

A halin yanzu dai Lord Triesman ya nemi afuwa daga hukumomin kwallon kafa na kasashen Rasha da Spaniya