Rezai ta doke Venus Williams a tennis

Aravane Rezie
Image caption Aravane Rezai ta lashe gasar Madrid open

'Yar kasar Faransa Aravane Rezai ta doke Venus Williams daci 6-2 7-5 inda ta lashe gasar tennis ta Madrid Open.

Rezai ta samu galaba akan Williams ne bayan sun shafe sa'a daya da minti 42 suna kece raini.

Wannan ne karo na uku da Rezai take daga kofin gasar tennis bayan ta samu nasara a bara a gasar Strasbourg data Bali.