Beckham ya mika bukatar Ingila ga FIFA

Beckham ya mikawa Blatter Bukatar Ingila
Image caption Beckham ya mikawa Blatter Bukatar Ingila

Shahararen dan wasan Ingila din nan, David Beckham ya mika bukatar Ingila mai shafi 1,752 na neman damar daukar bakonci gasar kwallon kafa na duniya da za a yi a shekarar 2018.

Hukumar FIFA za ta bayana kasar da za ta dauki bakoncin gasar cin kofin duniya na shekarar 2018 da 2022 a ranar biyu ga watan disamban wanan shekarar.

Kasar Rasha da kuma Australia na cikin jerin kasashen da suke neman daukar bakonci gasar.

"Muna matukar son kwallon kafa, kuma kwallon kafa abune da ke jini mu". Inji David Beckham a lokacin da yake mikawa Sepp Blatter Shugaban hukumar FIFA bukatar Ingila a birnin Zurich.

Kasashen tara ne dai suke neman damar daukan bakonci gasar cin jkofin duniya da za a yi a shekarar 2018.