Chelsea za ta kara da Portsmouth a wasan karshe na gasar FA

Chelsea
Image caption Tuni dai Chelsea ta lashe gasar Premier ta bana

Chelsea za ta kara da Portsmouth a wasan karshe na gasar cin kofin FA a filin wasa na Wembley a ranar asabar.

Ita dai Chelsea tana kokarin lashe kofinne don ya zama na biyu a cikin jerin kofinnan data lashe a kakar wasa ta bana.

Haka zalika, Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya zaku 'yan wasanshi su samu galaba a lokacin wasan, don ya shiga cikin jerin kocakocan da suka lashe manyan kofinna biyu a Ingila wato na gasar premier dana FA.

Ana saran John Terry ne zai jagoranci sauran 'yan wasan a wannan karawar.

A daya bangaren dai Portsmouth wacce ke kokarin kare kofin data lashe a bara na dauke da 'yan wasan Najeriya biyu wato Kanu Nwankwo da kuma John Utaka.

kuma za su maida hankali ne wajen jikawa Chelsea gari duk da cewar Portsmouth din ta bar gasar premier ta koma gasar Championship, sannan kuma tana fama da dibbin bashi akan ta.