Zan dade a Chelsea-Carlo Ancelotti

Ancelotti
Image caption Carlo Ancelotti ya lashe kofina biyu a shekararshi ta farko a Ingila

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya ce yanason ya cigaba da kasancewa tare da kungiyar daga nan har zuwa shekaru goma masu zuwa, bayan ya jagoranci kungiyar ta lashe kofina biyu a bana.

Ancelotti na bukatar zaman na lokaci mai tsawo ne a Stamford Bridge bayanda ya zamo kocinta na biyar cikin watanni 21.

Yace "idan har kowacce kakar wasa zata zama irin wannan, zanso in cigaba da zama daga nan har shekaru goma masu zuwa, kuma a shirye na in kulla wata sabuwar yarjejeniya".

Ancelotti wanda ya shafe shekaru takwas a kungiyar AC Milan a matsayin koci, ya kara da cewar: "ina son rayuwa a Ingila kuma akwai saukin jagoranci sosai a Chelsea.