Ballack ba zai je gasar kwallon kafa na duniya ba

Micheal Ballack
Image caption Kyaftin din Jamus, Micheal Ballack

Kyaftin din kasar Jamus, kuma dan wasan Chelsea, Micheal Ballack ba zai taka leda ba a gasar kwallon kafa da za yi a kasar Afrika ta kudu bayan raunin da ya samu.

Dan wasan dai ya samu raunin ne a wasan karshe da Chelsea ta buga a gasar cin kofin FA da Portsmouth a karshen makon daya gabata.

An dai gwada raunin ne a yau, inda kuma aka lurra cewa dan wasan ba zai samu sauki da wuri ba, har ya taka leda a gasar cin kofin duniya.