Bayern ta gamu da cikas akan Ribery

Ribery
Image caption Lokacin da alkalin wasa ya kori Ribery kenan.

Kotun sauraron karrarakin wasanni ta ce ba zai yiwu ba dan wasan Bayern Munich Frank Ribery ya buga wasan karshe na gasar zakarun turai tsakaninsu da Inter Milan a ranar Asabar.

A ranar litinin ne aka saurari daukaka karar da kungiyar Bayern Munich tayi akan dage dan wasan na tsawon wasanni uku, amma dai kotun ta ce hukuncin da hukumar UEFA ta yanke a zaune yake.

Wata sanarwa daga kotu ta ce " mun kori karar da Bayern Munich ta shigar akan dagewar da hukumar UEFA ta yiwa Ribery".