Zenden zai kara shekara a Sunderland

Zenden
Image caption Zenden ya dade ana damawa dashi a gasar premier

Dan wasan Sunderland Boudewijn Zenden ya sabunta yarjejeniyarshi da kungiyar na karin shekara guda.

Dan shekaru talatin da uku da haihuwa,Zenden ya koma Sunderland ne daga Marseille a watan Oktoban bara.

Kocin Sunderland Steve Bruce ya ce "munyi murna ganin cewar Zenden ya amince ya cigaba da kasancewa tare damu".

Ya kara da cewar dan wasan yanada kwarewa kuma muna bukatar irinsu don kara karfin klub dinmu.

Zenden ya taba taka leda a Chelsea da Middlesbrough a baya lokacin da yayi tamaula a Ingila.