Ingila ta cancanci shirya gasar kwallo

Capello
Image caption Kocin Ingila Fabio Capello

Fabio Capello ya ce yayi amanna Ingila nada dama sosai a matsayin kasar da zata dauki bakuncin gasar cin kofin duniya, duk da irin kace nacen da akeyi akan kalaman Lord Triesman.

Triesman ya sauka daga mukamin shugaban kwamitin daukar bakuncin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2018 ne bayanda ya zargi jami'an Spaniya da Rasha akan batun cin hanci.

Capello yace banji dadin abinda ya faru ba, amma yanzu zamu maida hankali don cigaban kanmu anan gaba.

A cewar Capello"batun neman daukar bakuncin yafi karfin mutum guda, saboda haka wasu zasu zo wasu kuma su tafi, amma daga karshe zamu samu nasarar daukar bakuncin gasar cin kofin duniya".