Barcelona na farautar Fabregas

Fabgregas
Image caption Fabregas yana son ya kwace kwallo daga wajen dan Barca Lionel Messi

Barcelona na farautar kaptin din Arsenal Cesc Fabregas, tun bayanda dan wasan ya bayyana cewar yanason komawa taka leda a Nou Camp.

A makon daya gabata ne Fabregas dan shekaru ashirin da uku da haihuwa wanda ya koma Arsenal daga Barca a shekara ta 2003, ya ce idan har ya bar Arsenal to Barca zai koma.

Shugaban kungiyar Barca Joan Laporta ya ce "abin jin dadi ne kalaman da dan wasan ya fada, saboda haka zamu tuntubi Arsenal akan batun".

Haka zalika, Barcelona na gabda kulla yarjejeniya da dan wasan Valencia David Villa.

A 'yan watanni masu zuwa ne wa'adin mulkin Laporta zai kare a matsayin shugaban Inter Milan, kuma mutane biyu dake harar kujerarshi wato Sandro Rosell da Alfons Godall duk sun bayyana sayen Fabregas a matsayin kampe dinsu.

A baya dai Fabregas tare da Lionel Messi sun taka leda a karamar kungiyar Barca kafin ya koma Arsenal.