FIFA ta sauya doka akan bugun penariti

Blatter
Image caption Shugaban hukumar FIFA Sepp Blatter

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta amince da sauya dokarta akan yadda za a dinga bugun penariti a gasar cin kofin duniya da za a fara a wata mai zuwa.

Sabuwar dokar ta haramtawa 'yan wasa 'yar tsayawan da suke yi kafin su buga kwallon.

A cewar FIFA din duk dan wasan da yayi haka za a bashi katin gargadi mai launin ruwan kyau, sannan kuma idan har kwallon ta shiga raga to za a kara bugawa.

Manufar 'yan wasa na tsayawa su kada gola kafin bugun shine don su batar da golan su samu nasarar zira kwallon a raga.