Gary Neville ya kalubalanci Capello

Neville
Image caption Gary Neville bai gamsu ba akan zaben 'yan wasan Ingila

Dan wasan Manchester United Gary Neville ya kalubalenci kocin Ingila Fabio Capello game da yadda ya zabi dan wasan Liverpool Glen Johnson a matsayin dan wasanshi tilo dake buga wasa ta baya a bangaren dama.

Neville yace "naji mamaki ace mutum daya ne kadai yake buga bangaren dama a baya".

Ya kara da cewar ba daidai bane Capello ya nemi dawo da Paul Scholes cikin tawagar Ingilan.

Bayan da bukatar Capello akan Scholes yaki aiki, sai ya shawokan dan wasan Liverpool Jamie Carragher da cewar ya koma bugawa Ingila duk da cewar shekaru uku da suka wuce ya sanarda cewa yayi ritaya.