Milner yafi darajar pan miliyan 20

Milner
Image caption Milner ya kasance matashin dan kwallo dake tashe a Ingila

Aston Villa ta ki amincewa da tayin pan miliyan ashirin akan dan wasanta James Milner daga wajen Manchester City.

Kakakin kungiyar Villa ya bayyana cewa sun ki karbar tayin da Manchester City tayi akan Milner saboda kudaden sunyi kadan.

Ya kara da cewar "mun shirya zama tare da James da wakilinshi bayan an kamalla gasar cin kofin duniya don mu tattauna yadda yarjejeniyar zata kasance".

Milner dan shekaru ashirin da hudu a kwanan aka bashi kyautar gwarzon dan kwallon matasa na bana a Ingila.

Milner dai ya koma Villa ne daga kungiyar Newcastle a shekara ta 2008 akan pan miliyan 12, sannan kuma yana cikin jerin 'yan wasa talatin da Ingila ta gayyata don fara horo a shirye shiryenta na tunkarar gasar cin kofin duniya.