Mourinho ya soki gasar cin kofin duniya

Mourinho
Image caption Wasu na hasashen cewar Mourinho zai koma Real Madrid

Kocin Inter Milan Jose Mourinho ya ce gasar cin kofin zakarun Turai tafi gasar cin kofin kasashen duniya girma da armashi.

Mourinho wanda kungiyarshi zata kara da Bayern Munich a wasan karshe na gasar a ranar Asabar mai zuwa yace baida tantama haka lamarin yake.

Yace "A raayina shine wasan da yafi mahimanci, shine wasan kwallo dayafi mahimmanci a doron kasa, wanda kuma yafi gasar cin kofin duniya mahimanci, saboda yadda ake murza leda a gasar,kuma klub klub sun fi kasashen zaratan 'yan kwallo".

Da dama dai an jinjinawa Mourinho akan irin dabarunshi yadda ya doke Barcelona a wasan zagayen kusada karshe kuma a lokacin wasan Lionel Messi ya kasa wani matabus.