Robben ya soki salon Mourinho

Robben da Mourinho
Image caption Arjen Robben tare da Mourinho a Chelsea

Dan wasan Bayern Munich Arjen Robben ya ce tsohon kocinshi a Chelsea Jose Mourinho yafi maida hankali wajen samun nasara a wasa amma bai damu da salon wasan 'yan kwallonshi ba.

Robben zai fuskanci tsohon kocinshi a wasa tsakanin Munich da Inter Milan na karshe a gasar zakarun Turai a ranar Asabar.

Robben yace"zamu nemi samun nasara koda kwallon yayi dadi ko beyi ba".

Bayanda Inter Milan ta kasa tsallakewa daga zagayen farko a shekaru biyu a jere, Mourinho ya kai Inter Milan zuwa wasan karshe a karon farko cikin kusan shekaru 40.