Berbatov ba na siyarwa bane - Inji Ferguson

Dimitar Berbatov
Image caption Dimitar Berbatov

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce kungiyar bata da niyar siyarda dan wasan gabanta Dimitar Berbatov.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 29 bai taka rawar gani ba a kakar wasan data gabata bayan Manchester ta siye shi a fam milin talatin daga kungiyar Tottenham a shekarar dubu biyu da takwas.

Amma Ferguson ya ce bashi da niyar rabuwa da dan wasan.

"Kwararren dan wasa ne kuma na tabbatar muku cewar zai buga wasa da mu a kakar wasa na badi". Inji Ferguson.

Kungiyoyi kamarsu Bayern Munich da AC Milan da Tottenham suna nema siyan dan wasan.