Dangote na son sayen wani kaso a Arsenal

Dangote
Image caption Mujallar Forbes ta Amurka ta bayyana Aliko Dangote a matsayin wanda yafi arziki a Afrika.

Rahotanni sun nuna cewar hamshakin dan kasuwa a Najeriya, Alhaji Aliko Dangote yana da muradin siyen kashi goma sha shida cikin dari na hannun jari a Arsenal da Nina Bracewell-Smith tasa a kasuwa.

Jaridar Sunday Times ta bayyana cewar kamfanin Blackstone ce tayi rajistar Dangote a cikin wadansa suka nuna sha'awar siyen kason.

Ita dai Nina Bracewell-Smith na bukatar pan miliyan 160 ga duk wanda yake son mallakar kashi 16 dake hannunta.

Bayaga Dangote dai Stan Kroenke da Alisher Usmanov wadanda keda kaso mafi tsoka a kungiyar ta Arsenal suma sona kwadayin sayen kashi sha shidan.

Rahotannin sun ce Dangote na sha'awar kwallon kafa kuma yana da arzikin da zai iya goggayya da sauran mutane biyu.