Yakamata Ingila ta lashe kofin duniya

Gerrard
Image caption Steven Gerrard na tunanin barin Liverpool

Steven Gerrard ya amince cewar lokaci ya fara kurewa manyan 'yan wasan Ingila idan har basu lashe gasar cin kofin duniya ba a bana.

Gerrard me shekaru 30 na daga cikin 'yan wasan Ingila da dama wadanda suka yi suna a duniya kuma zasu taka leda a gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu.

Dan wasan na Liverpool ya ce"Ina tunanin cewar wannan ne gasar cin kofin duniya ta karshe a wajenmu saboda haka dole ne mu kafa tarihi".

Kaptin din Ingila Rio Ferdinand da Frank Lampard suma dai sun wuce shekaru 30, a yayinda John Terry da Ashley Cole su kuma ke kan hanya.

A jawabinshi can a sansanin horon 'yan wasan Ingila dake kasar Austria, Gerrard ya kara da cewar"Shekaru talatin lokaci ne da zaka yi kokarin cimma burinka a kasarka".