Rodwell zai cigaba a Everton har zuwa 2015

Rodwell
Image caption Jack Rodwell sune manyan gobe a Ingila

Dan wasan tsakiya na Everton Jack Rodwell ya sanya hannu a sabuwar yarjejeniya ta karin shekaru biyar tare da kungiyar.

Dan shekaru 19 da haihuwa, Rodwell a baya an alakantashi da Manchester United akan pan miliyan goma sha biyar, amma a yanzu yace zai cigaba da kasancewa karkashin David Moyes.

Rodwell ya fara bugawa Everton leda ne a watan Disamban 2007 yana dan shekaru 16.

Ya kulla yarjejeniyar farko a watan Fabarairu na 2009 inda ya haskaka a kakar wasan bana abinda yasa kungiyar ta nemi ya tsawaita zamanshi da ita.