An bude filin wasa a kasar Afrika ta kudu

The Calabash
Image caption Babban filin wasa na Soccer City 'The Calabash'.

Sama da 'yan kallo dubu saba'in da hudu ne suka halaraci babban filin wasa na Soccer City inda za a buga wasan karshe a gasar cin kofin duniya da za'a yi a kasar Afrika ta kudu.

An dai buga wasan karshe ne na cin kofin Afrika ta kudu a filin, ana sauran makwanni hudu a fara gasar cin kofin duniya.

Kungiyar Johannesburg's Bidvest ce ta doke kungiyar Amazulu ta Durban da ci uku a nema a wasan.

An siyarda tikitin shiga filin wasan gabaki daya duk da cewa dai, kungiyoyin biyu ba sa tasiri a kasar.

Filin wasa wanda aka lakabawa suna 'The Calabash', shine filin wasa mafi girma a nahiyar Afrika

Idan an fara gasar cin kofin duniya ana sa ran filin wasan zai dauki 'yan kallo da yawansu zai kai dubu casa'in da biyar.