Aruna Dindane ya koma Lekhwiya ta Qatar

Aruna Dindane
Image caption Dan kwallon Ivory Coast Aruna Dindane

Tsohon dan wasan Portsmouth kuma dan Ivory Coast Aruna Dindane ya koma kungiyar Lekhwiya ta kasar Qatar.

Dan shekaru ashirin da tara da haihuwa, Dindane ya zira kwallaye takwas a lokacin yana takawa Portsmouth leda bayan da ta dauki aronshi na shekara guda daga Lens ta Faransa.

Ya dai fuskanci matsaloli a lokacin da Portsmouth ta dauki aronshi, saboda ta kasa biyanshi kudinshi wato pan miliyan uku da rabi, inda Porstmoth din ta bukaceshi ya buga mata kwallo ba tare da ta biyashi ba.

Dan kwallon Ivory Coast din ya taikamawa Portsmouth ta kai wasan karshe na gasar cin kofin FA a Ingila bayanda ya samu fenaritin da Kevin Prince Boateng ya ci inda aka tashi biyu da nema tsakaninsu da Tottenham a wasan kusada karshe.