Ingila ta doke Mexico a wasan sada zumunci

Yan wasan Ingila
Image caption Yan wasan Ingila

A shirye shiryenta na halartar gasar cin kofin duniya da za yi a Kasar Afrika ta kudu, Ingila ta buga wasan sada zumunci da Mexico a filin wasa na Wembley, inda ta doke Mexico da ci uku da guda.

Dan wasan bayan Ingila Ledley King ne ya fara zura kwallon farko, sannan kuma Peter Crouch ya zura ta biyu.

Kafin a tafi hutun rabin lokaci ne dai dan wasan Mexico, Guillermo Franco ya fanshe wa kasar kwallo guda.

Bayan an dawo hutun rabin lokaci ne kuma Glen Johnson ya zura kwallo ta uku.

Ingila dai za ta buga wasanta na farko ne da kasar Amurka a ranar 12 ga watan Yuni a gasar cin kofin duniya da za a yi a kasar Afrika ta kudu.