Mourinho ya kammala aikinshi a Inter

Mourinho
Image caption Jose Mourinho koci ne da ake girmamawa a duniya

Shugaban kungiyar Inter Milan Massimo Moratti yace kocin kungiyar Jose Mourinho ya kammala aikinshi a Inter bayan lashe gasar zakarun Turai.

Massimo Moratti ya shaidawa kamfanin dillancin labarai a Italiya mai suna Ansa cewar Mourinho ya riga ya yanke shawarar komawa Real Madrid wacce ta kamalla kakar wasan data wuce babu kofi.

A halin yanzu dai ajen din Mourinho ya riga ya tattauna da shugabanin Real Madrid akan batun canza shekar.

Wata jarida a Spaniya Marca ta bayyana cewar Mourinho zai kulla yarjejeniya ta tsawon shekaru hudu a Real inda ako wacce shekara za a iya bashi dala miliyan goma sha biyu da rabi.