West Ham ta fasa baiwa Najeriya filinta

Super Eagles
Image caption 'Yan wasan Super Eagles na Najeriya

Najeriya ta sauya filin wasan da zata kara da kasar Columbia na ranar 30 ga watan Mayu, bayan da kungiyar West Ham ta Ingila ta fasa bada naya filinta don ayi karawar.

Yanzu dai za a buga wasan ne a filin Luton Town's Kenilworth Road ground.

Kakakin hukumar kwallon Najeriya NFF Ademola Olajire ya shaidawa BBC cewar wannan ba karamar matsala bace a shiryen shiryen Super Eagles na fuskantar gasar cin kofin duniya.

Ya kara da cewar "muna neman afuwa daga dinbim magoya bayan super eagles wadanda suka riga suka kamalla shirye shiryen zuwa kallon wasan a London".

Najeriya zata kara da Saudi Arabiya a kasar Austria a ranar Talata kafin su koma sansanin horonsu dake Essex a Ingila.