Har yanzu Masar ce ta farko a fagen kwallon Afrika

'Yan wasan Masar da Najeriya
Image caption 'Yan wasan Masar na karawa da Najeriya

Masar wacce ba zata buga gasar cin kofin duniya ba , har yanzu itace ta farko a Afrika a fagen kwallon kafa amma ta 12 a duniya.

Amma dai mai masaukin bakin gasar cin kofin duniya a bana Afrika ta Kudu ta yinkuro inda ta zama ta 83 a duniya sabbanin ta 90 a watan daya gabata.

A ranar laraba ne dai hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta fidda jerin kasashen da suka yi zarra a fagen kwallon kafa a wannan lokacin.

Sai dai a duniya Brazil ce ta farko sai Spaniya ta binta a baya sai Portugam ta uku.

Goman farko a Afrika:

1. Masar (12 a duniya)

2. Cameroon (19 a duniya)

3. Nigeria ( 21 a duniya)

4. Ivory Coast (27 a duniya)

5. Algeria (30 a duniya)

6. Ghana (32 a duniya)

7. Gabon (42 a duniya)

8. Burkina Faso (48 a duniya)

9. Mali (54 a duniya)

10. Tunisia (55 a duniya)