FIFA zata samar da karin tikiti 150,000

Sepp Blatter
Image caption Shugaban hukumar FIFA Sepp Blatter

Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, ta bayar da sanarwar cewa zata samar da karin tikiti na shiga kallon wasan kwallon kafa na duniya guda dubu dari da hamsin.

Lokacin da yake jawabi wajen mika ragamar harkar wasan a birnin Cape Town, Sakatare Janar na hukumar Jerome Valcke, ya ce za a fara sayar da karin tikitin da hukumar zata samar ranar juma'a.

Hukumar ta ce karin sayar da tikitin zai kara bunkasa yawan wadanda za a sayarwa zuwa miliyan biyu da rabi.