Real Madrid ta kori kocinta Manuel Pellegrini

Pellegrini
Image caption Tsohon kocin Real Madrid Manuel Pellegrini

Kungiyar Real Madrid ta Spaniya ta kori kocinta Manuel Pellegrini a yayinda take shirin nada daya daga cikin masu horar da 'yan wasa mafiya kwarewa wato Jose Mourinho ya zama sabon kocin Kulob din.

Kulob din na Real Madrid yace za a kammala yarjejeniya ne da zarar Mr Mourinho, wanda ke kallon kasa wani kociya na musamman ya gamma tattaunawa da kulob dinsa na yanzu wato Inter Milan.

Tun bayan da Mourinho ya lashe gasar zakarun Turai aketa maganar zai koma Spaniya.

Shugaban kungiyar Real Madrid Florentino yace "na shirya amince mun tafka kura kurai,amma dai daukar mourinho wata dama ce da bazamu bari tawuce me ba".

Amma dai shugaban Inter din Massimo Moratti ya bayyana cewar idan har Mourinho zai tafi to za ayi jan- in- ja don kuwa sai an basu diyyar pan miliyan 13 da rabi saboda kamata yayi Mourinho ya barsu a shekara ta 2012.