Micheal Essien ba zai je Afrika ta Kudu ba

Essien
Image caption 'Yan Ghana suna bakin cikin jin labarin raunin Essien

Hukumar kwallon Ghana ta sanarda cewa dan wasanta Micheal Essien ba zai buga gasar cin kofin duniya ba.

Dan wasan dai yana fama da rauni kuma sai a karshen watan Yuli ne zai warke.

Hukumar kwallon Ghanan ta ce ta dauki wannan hukuncin ne bayan tayi nazarin yanayin ciwon da dan wasan yake jinya.

Tun a watan Junairu lokacin gasar cin kofin kasashen Afrika a Angola rabonda Essien ya shafa leda.

Wannan batun dai ba karamin cikas zai kawo ma Ghana ba , ganin cewar Essien na daga cikin zaratan 'yan wasan data ke ji da su.

Ghana na rukunin d ne a gasar cin kofin duniya tare da kasashen Jamus da Australia da Serbia.