Holland ta fidda jerin 'yan wasanta 23

'Yan wasan Holland
Image caption Holland bata kira Nistelrooy cikin tawagarta ba

Holland ta fidda jerin 'yan wasanta ashirin da uku wadanda zasu taka mata leda a Afrika ta Kudu.

Kocin kasar Bert van Marwijk ya sanarda jerin 'yan wasan ne a ranar Alhamis inda ya fidda 'yan wasa hudu daga cikin wadanda ya kira da farko.

Holland dai na rukunin E ne a gasar cin kofin duniya tare da kasashen Denmark da Japan da kuma Kamaru.

'Yan wasan da kungiyoyin da suke takawa leda:

Maarten Stekelenburg (Ajax), Sander Boschker (FC Twente), Michel Vorm (FC Utrecht); Khalid Boulahrouz (Stuttgart), Edson Braafheid (Celtic), Giovanni van Bronckhorst (Feyenoord), John Heitinga (Everton), Joris Mathijsen (HSV), Gregory van der Wiel (Ajax), Andre Ooijer (PSV); Mark van Bommel (Bayern Munich), Nigel de Jong (Manchester City), Stijn Schaars (AZ), Wesley Sneijder (Inter), Rafael van der Vaart (Real Madrid), Demy de Zeeuw (Ajax), Ibrahim Afellay (PSV); Dirk Kuyt (Liverpool), Eljero Elia (HSV), Ryan Babel (Liverpool), Klaas-Jan Huntelaar (AC Milan), Robin van Persie (Arsenal), Arjen Robben (Bayern Munich).