Lampard ba zai koma Real Madrid ba

Lampard
Image caption Frank Lampard na daga cikin 'yan wasan da ake girmamawa a Chelsea

Shugaban kungiyar Chelsea Bruce Buck ya ce dan wanshi Frank Lampard ba zai koma Real Madrid ba.

Rahotanni sun nuna cewar tsohon kocin Chelsea kuma mai horadda 'yan wasan Real Madrid a yanzu Jose Mourinho na zawarcin Lampard don ya shiga cikin 'yan wasanshi a Madrid.

Mourinho da Lampard sun fahimci juna sosai a lokacin da Mourinho ya shafe shekaru uku yana Chelsea.

Lampard dai ya bayyana cewar yana sha'awar komawa inda Mourinho yake.