Najeriya ta fitar da jerin 'yan wasanta da za su Afrika ta Kudu

Osaze Odemwingie
Image caption Dan wasan Najeriya Osaze Odemwingie a fagen fama

Kocin Najeriya Lars Lagerback ya fitar da jerin sunayen 'yan wasan da za su taka wa kungiyar Super Eagles kwallo a gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu.

'Yan wasan dai ba su kunshi Ikechukwu Uche da yake buga wa kungiyar Real Zaragoza, da kuma dan wasan kulob din Everton Victor Anichebe.

Sai dai abokin wasan Anichebe a kulob din Everton Joseph Yobo, da Kanu Nwankwo da kuma dan wasan kulob din Chelsea Mikel obi duk sun samu shiga.

Mikel Obi dai na ci gaba da murmurewa ne daga ciwon da ya samu a kwauri, kuma ya hade da sauran 'yan wasan ne a ranar Juma'a.

Sauran 'yan wasan da za su je kasar ta Afrika ta kudu sun hadar da John Utaka, da Yakubu Aiyegbeni na kulob din Everton, sai Dickson Etuhu na kulob din Fulham da kuma Danny Shittu na kulob din Bolton.

Najeriya tana rukunin B ne a gasar ta cin kofin duniya. Rukunin ya kuma kunshi kasashen Argetina da Greece da kuma kasar Koriya ta Kudu.

Kungiyar Super Eagles ta Najeriya za ta kara wasanta na farko ne a ranar 12 ga watan Yuni. Najeriyar za ta kara ne da kasar Argentina, a wasan da ake ganin zai ja hankalin mutane da dama a duniya.

Jerin sunayen 'yan wasan Najeriya

Masu tsaron gida

 • Vincent Enyeama
 • Dele Aiyenugba
 • Austin Ejide

'Yan wasan baya

 • Taye Taiwo
 • Elderson Echiejile
 • Chidi Odiah
 • Joseph Yobo
 • Daniel Shittu
 • Ayodele Adeleye
 • Rabiu Afolabi

'Yan wasan tsakiya

 • Chinedu Oguke Obasi
 • John Utaka
 • Kalu Uche
 • Dickson Etuhu
 • John Mikel Obi
 • Sani Kaita
 • Haruna Lukman
 • Yusuf Ayila
 • Osaze Odemwingie

'Yan wasan gaba

 • Yakubu Aiyegbeni
 • Nwankwo Kanu
 • Obafemi Martins
 • Victor Obinna Nsofor