Takaitaccen Tarihin Kwallon Australia

Australia
Image caption Wasu 'yan wasan Australia

Wannan ne dai karo na uku da Australia za ta buga gasar cin kofin duniya, bayan da aka fafata hadda ita a shekarar 1974 da kuma 2006.

A lokacin wasannin share fage na cancantar shiga cikin gasar da za ayi a kasar Afrika ta Kudu, Australia ta zama kasa ta farko daga yankin nahiyar Asiya data tsallake inda ta doke kasashe kamarsu Japan da China.

Sannan kuma sai da akayi wasanni bakwai ba a zira kwallo a ragarta ba.

Australia dai bata taba wuce zagaye na biyu ba a gasar cin kofin duniya, kuma a bana ta dogara ne akan manyan 'yan wasanta kamarsu Harry Kewell da Tim Cahill don ganin ta wuce wannan matakin.

Amma dai akwai babban kalubale akan kocin kasar Pim Verbeek gannin cewar a gasar da akayi a kasar Jamus na shekara ta 2006, Australia ta haskaka saboda itace ta zamo na biyu a rukuninta inda tabi bayan Brazil sannan kuma ta shiga gaban kasashen Croatia da Japan.

Australia na rukunin D ne tare da Jamus da Serbia da Ghana