Capello zai cigaba a Ingila zuwa 2012.

Capello
Image caption Kocin Ingila Fabio Capello

Kocin Ingila Fabio Cappello ya sanya hannu a yarjejeniyar cigaba da kasancewa da Ingila har zuwa shekara ta 2012.

Wannan sauyin dai na nufin cewar Capello ya fasa barin Ingila idan an kamalla gasar cin kofin duniya, kuma ya kawo karshen burin Inter Milan ta nada shi a matsayin mai horadda 'yan wasanta.

Capello yace " Ina murna akan wannan batun, kuma ina godiya ga hukumar kwallon Ingila data bani wannan damar".

Wannan matakin na tsohon kocin Real Madrid da AC Milan za ta karawa 'yan wasan Ingila karfin gwiwa a gasar cin kofin duniya.