Takaitaccen tarihin kwallon Italiya

Italiya
Image caption 'Yan kwallon Italiya

Italiya dai zata je Afrika ta Kudu a matsayin kasar da kuwa zai so yaga irin taka rawar ta saboda itace ke neman kare kofin data lashe a Jamus a shekara ta 2006.

A tarihi dai banda Brazil babu kasar data lashe gasar cin kofin duniya sau biyu a jere, amma dai Italiya tayi hakan a shekarar 1934 da 1938.

A kan hanyar ta na zuwa Afrika ta kudu dai Italiya ta samu nasara a wasanni 7 ta kuma yi canjaras a wasanni uku inda ta zira kwallaye 18, aka kuma zira mata 7.

'Yan wasan da zasu jagoranci Italiya a bana sune gola Gianluca Buffon da Fabio Canavaro da kuma Gennaro Gattuso.

A baya dai Italiya ta lashe gasar cin kofin duniya har sau hudu, kuma a bana karkashin kocinsu Marcello Lippi, Italiya dai zata neman daga kofinta na bayar.

Italiya dai an santa da adana tsaffin 'yan wasa, kuma a bana ba yawancin 'yan kwallonta na gasar da akayi a shekara ta 2006 sune zasu wakilce ta.

A Afrika ta Kudu dai Italiya na rukunin Fa tare da kasashen Paraguay da New Zealand da Slovakia.