Takaitaccen tarihin kwallon Japana

Japan
Image caption Tawagar 'yan kwallon Japan

Ana kallon kasar Japan a matsayin wacce ta fi karfi a yankin nahiyar Asiya kuma wannan ne karo na hudu da zata buga gasar cin kofin duniya.

Japan dai bata fusknaci wata matsala ba akan na hanyar ta zuwa Aftika ta kudu inda ta samu nasara a wasann hudu ta tashi canjaras a uku aka doke ta a daya.

Japan dai zata dogara ne akan manyan 'yan wasanta biyu dake taka leda a Turai wato Shunsuke Nakamura da kuma Keisuke honda don taka rawar gani a Afrika ta kudu.

Japan dai bata taba wuce zagaye na biyu ba a gasar cin kofin duniya inda a shekara ta 2002 kasar Turkiya ta fidda ita a gasar.

A can nahiyar Asiya dai Japan ta kasance kasar da za a kalla a kuma kalla saboda ta lashe gasar cin kofin kasashe Asiya sau uku cikin shekaru biyar din da suka wuce.

Babban kalubalen dake gaban kocin kasar Supremo Okada shine haskaka a duniya kamar yadda yake yi a nahiyarsu.

Japan dai na rukunin E ne a gasar da za ayi a Afrika ta kudu tare da kasashen Denmark da Holland da kuma Kamaru.