Babu McCarthy a tawagar Afrika ta Kudu

Tawagar Afrika ta Kudu
Image caption Akwai kalubale a gaban 'yan wasan Afrika ta Kudu

Kociyan Afrika ta Kudu Carlos Alberto Parreira, ya ajiye dan wasan West Ham Benni McCarthy daga cikin jerin 'yan wasa 23 da zai yi amfani da su a gasar cin kofin duniya. Dan wasan mai shekaru 32, yafi kowa zira kwallaye a kasar, sai dai yayi fama da rashin lafiya.

Steven Pienaar na Everton da Kagiso Dikgacoi na Fulham na daga cikin wadanda suka samu shiga.

Aaron Makoena na Portsmouth wanda ya zamo dan kasar na farko da ya buga wasa 100, a karawar da suka yi da Guatemala ranar Litinin, shi ma ya samu shiga.

Kasar ce dai mai masaukin baki, kuma za ta kara a rukunin A da Mexico da Uruguay da Faransa.

Jerin 'yan wasa 23 na Afrika ta Kudu

Masu tsaron gida: Moeneeb Josephs (Orlando Pirates), Itumeleng Khune (Kaizer Chiefs), Shu-Aib Walters (Maritzburg United)

'yan baya: Matthew Booth, Siboniso Gaxa (both Mamelodi Sundowns), Bongani Khumalo (SuperSport United), Tsepo Masilela (Maccabi Haifa), Aaron Mokoena (Portsmouth), Anele Ngcongoa (Racing Genk), Siyabonga Sangweni (Lamontville Golden Arrows), Lucas Thwala (Orlando Pirates).

'yan tsakiya: Lance Davids (Ajax Cape Town), Kagisho Dikgacoi (Fulham), Thanduyise Khuboni (Lamontville Golden Arrows), Reneilwe Letsholonyane (Kaizer Chiefs), Teko Modise (Orlando Pirates), Surprise Moriri (Mamelodi Sundowns), Steven Pienaar (Everton), MacBeth Sibaya (Rubin Kazan), Siphiwe Tshabalala (Kaizer Chiefs).

'yan gaba: Katlego Mphela (Mamelodi Sundowns), Siyabonga Nomvete (Moroka Swallows), Bernard Parker (FC Twente).