'Yan Super Eagles suna tsaka me wuya a London

Super Eagles
Image caption 'Yan wasan Super Eagles na Najeriya

Tawagar 'yan kwallon Najeriya sun fuskanci matsalar jirgin sama a London abinda ya kawo musu tsaiko akan hanyarsu ta zuwa Afrika ta Kudu.

A bisa tsari dai a daren ranar litinin ne 'yan Super Eagles din ya kamata su bar Ingila su koma Afrika ta Kudu.

Tawagar Super Eagles dai ta shafe lokaci mai tsawo a filin jirgin sama na Stansted saboda matsalar da jirgin nasu ya samu.

Gwamnatin Najeriya dai ta bada umurnin aikewa da sabon jirgin sama daga birnin Paris don dauke 'yan wasan zuwa Afrika ta Kudu.