Takaitaccen tarihin Algeriya

Tawagar 'yan wasan Algeriya
Image caption Tawagar 'yan wasan Algeriya na fatan taka rawar gani a gasar ta bana

Shekaru 24 kenan rabon Algeria da taka leda agasar cin kofin duniya, abinda yasa 'yan kasar dama 'yan wasan baki daya, ke azarbabin ganin anfara gasar ta bana.

Algeria ta fuskanci kalubale akan haryar ta ta zuwa Afriak ta kudu, wasan kifa daya kwalen data buga da Masar ya jefa kasashen biyu cikin rudani.

Sun ta shi dai dai da dai dai ta Masar a rukuni na biyu, amma ta yi nasar doke Masar din awasan kifa daya kwalen da suka buga a Sudan.

Kasar ta taka rawar gani agasar cin kofin Afrika da aka buga a Angola, inda ta kai wasan kusa dana karshe.

Manyan 'yan wasan da kasar za ta dogara da su sun hada da Antar Yahia da Majdid Boughera da Nadir Belhadj da kyaftin Yazid Mansouri.

A kawai babban kalubale a gaban mai horas da 'yan wasa Rabah Saadane, ganin cewa wannan shi ne karo na uku da kasar ke halattar irin wannan gasa.

A shekara ta 1982, Algeria ta taka rawar gani inda ta doke West Germany daci 2-1, sannan da lashe Chile daci 3-2.

Amma ta taka mummunar rawa a shekarar a 1986, inda ta sha kashi a hannun Brazil da Spain, sannan tayi kunnen doki da Ireland ta arewa.