Takaitaccen tarihin Argentina

'yan wasan Argentina
Bayanan hoto,

Jama'a na jinjinawa 'yan kwallon Argentina

Duk da cewa Argentina bata taka rawar gani a wasannin share fage ba, masu lura da al'amura na yi mata kallon daya daga cikin kasashen da ka iya taka rawar gani, ganin irin shahararrun 'yan wasan da Allah ya albarka ceta da su.

Yau kusan shekaru 24 kenan rabon da kasar da ta lashe gasar cin kofin duniya, abinda kociyan kasar Diego Maradona yace shi ne burin sa.

Argentina ta sha wuya akan hanyarta ta zuwa Afrika ta Kudu, inda bata samu kanta ba sai a zagayen karshe, inda ta sha da kyar a hannun Peru da Uruguay.

Shahararrun 'yan wasan da kasar za ta dogara da su sun hada gwarzon dan kwallon duniya Lionel Messi na Barcelona da Diego Milito, wanda ya taimakawa Inter Milan ta lashe gasar zakarun turai.

Da Sagio Aguiro na Atlethico Madrid da tsohuwar zuma Juan Sebastian Veron.

A gasar ta bana dai kasar za ta kare ne a rukuni guda da Najeriya da Girka ta kuma Jamhuriyar Koriya.

Tarihi ya nuna cewa Argentina ta taba lashe gasar cin kofin duniya a shekarun 1978 da 1986.

Sannan takai wasan karshe har sau biyu.

Fatan koc Diego Maradona shi ne na kasancewa a sahun wadanda suka taba lashe gasar a matsayin 'yan wasa, sannan suka maimaita a matsayin masu horas wa.