Takaitaccen tarihin Denmark

Tawagar Denmark
Image caption Tawagar Denmark ta zuwa Afrika ta Kudu

A 'yan shekarun da suka gabata dai ba'aji duriyar Denmark ba, kuma bayan shafe shekaru shida ana yi babu ita.

Kasar za ta yi fatan ganin ta taka rawa ta zo agani a gasar da za a fafata a Afrika ta Kudu.

Kasar Denmark ta taka rawar gani a gasar da ta halatta a baya, kuma ta yi ba zata akan hanyar ta ta zuwa Afrika ta Kudu, bayanda ta doke kasashen Portugal da Sweden.

Sau daya dai aka doke kasar awasannin share fagen da ta buga.

Kasar Denmark na da shahararrun 'yan wasa da dama wadanda ke taka leda a manyan kungiyoyin Turai.

Wadanda suka hada da Jondal Tomasson na Fayernood da Daniel Agger na Liverpool da Nicklas Bendtner na Arsenal.

Yau shekaru goma kenan da Koc Mortin Olsen ya shafe yana horas da 'yan wasan kasar, abinda yasa wasu ke ganin shi ne dalilan da yasa kasar ke taka rawar azo agani a 'yan kwanakinnan.

Kasar Denmark na rukunin E inda za ta kara da kasashen Halland da Kamaru da kuma Japan.