Takaitaccen tarihin kwallon Ivory Costa

Kyaftin din Ivory Cost Didier Drogba
Image caption Kyaftin din Ivory Cost Didier Drogba

Idan akwai wata kasar Afriaka da za ta karawar gani a gasar ta bana, to masana na hasashen Ivory Cost ce ganin irin kwararrun 'yan wasan da take da su.

Sai dai tana na da kalubale a gabanta ganin yadda ba tayi wani katabus a gasar da ta gabata ba.

Kasar bata fuskanci wata matsalaba a kan harya ta ta zuwa Afrika ta Kudu, inda babu wata kasa da tayi nasara akan ta.

Shahararrun 'yan wasan da za su jagoranci kasar sun hada da gwarzon dan kwallon kafa na Afrika Didier Drogba da takwaransa na Chelsea Solomon Kalou.

Da kuma Yaya Toure na Barcelona da Didier Zakora na Sevillla da Emmanuel Eboue na Arsenal da Kolo Toure na Manchester City.

Wani kalubale da ke gaban kociyan kasar Sven-Goran Erickson, shi ne na kasancewar sa sabo a kasar, ganin cewa 'yan watanni kadan kafin fara gasar aka nada shi, sai dai yayi alkawarin yin amfani da kwarewarsa wajen kai kasar ga gaci.

Za dai su kara ne da kasashen Brazil da Portugal da Koriya ta Arewa a rukunin G.

So daya dai kasar ta bata halattar wannan gasa a baya, kuma jama'a da dama na sa ido sosai akan ta, ganin irin shahararrun 'yan wasan da take da su.