Takaittacen tarihin Jamhuriyar Koriya

Tawagar Jamhuriyar Koriya
Image caption Tawagar Jamhuriyar Koriya

Jamhuriyar Koriya dai ta fi kowace kasa a nahiyar asiya halartar gasar cin kofin duniya da ake shiryawa. Kasar dai ta halarci gasar cin kofin duniya har sau bakwai a baya.

A hanyarta na cancantar taka leda a gasar cin kofin duniya, Jamhuriyar koriya ce ta jagoranci rukunin da ta buga.

Tarihi ya nuna cewa kasar ta fara halarta gasar cin kofin duniya ne a shekarar 1954, kuma bayan shi bata sake halartar wata gasar ba sai kuma wanda aka shirya a shekarar 1986.

Bayan wanan gasar ce kasar ta ci gaba da halarta sauran gasar da aka shirya. Jamhuriyar Koriya dai ta yi fice ne a gasar da aka shirya a kasar a shekarar dubu biyu da biyu, inda har ta kaiga buga wasan kusa dana karshe.

A wannan gasar dai, Jamhuriyar Koriya ta doke manyan kasashe kamarsu Portugal da Italiya da kuma Spaniya.

Dan wasan Manchester United Park Ji Sung ne kyaftin din tawagar kasar, kuma Huh Jung Moo ne zai jagoanci kasar a matsayin kocinta.