Takaittaccen tarihin Switzerland

Tawagar Switzerland
Image caption Tawagar Switzerland

Gasar da za a shirya a kasar Afrika ta kudu shine, ita ce karo na tara da kasar Switzerland za ta bakonci gasar cin kofin duniya.

Kasar dai ta lashe wasanni biyar ne a hanyarta na zuwa gasar cin kofin duniya, a yayinda ta buga canjaras a wasa guda kuma aka doke ta a wasa daya.

Switzerland dai ta kai matakin wasan dab da kusa dana karshe ne a gasar da aka shirya a shekarar 1934 da 1938 da kuma 1954. An dai fidda kasar ne a zagaye na biyu a gasar da ta halarta a 2006 a kasar Jamus.

Switzerland za ta halarci gasar ne da shahararen dan wasan ta Alexander Frie, wanda ke taka leda a kungiyar Basel da ke Switzerland. Kuma tsohon kocin Bayern Munich Ottmar Hitzfield ne zai jagoranci tawagar kasar zuwa Afrika ta kudu.

Siwtzerland dai za ta buga ne a rukunin H tare da kasar Spain da Honduras da kuma Chile.