Rafael Benitez ya bar Liverpool

Rafael Benitez
Image caption Rafael Benitez ya shafe shekaru shida a Liverpool

Kungiyar Liverpool ta bada sanarwar cewa ta raba aure tsakanin ta da Rafael Benitez, bayan da ya shafe shekaru shida a klub din.

Benitez, dan shekaru 50, ya maye gurbin Gerard Houllier a watan Junin shekara ta 2004, sannan ya jagorance su zuwa lashe gasar zakarun Turai.

Amma a kakar wasan data gabata, an fitar da su a farkon gasar, sannan suka kare a matsayi na shida a gasar Premier.

Manajin Darakta Christian Purslow da Manaja Kenny Dalglish, za su fara neman wanda zai jagoranci klub din.

Klub din yace babu wani wa'adi da yasa na nada sabon mai horas da 'yan wasa a klub din.

Masana sun dade suna hasashen cewa Rafael Benitez, ka iya barin Liverpool, saboda halin tsaka mai wuyar da kungiyar ta samu kanta a ciki.