Takaitaccen tarihin kwallon Girka

Takaitaccen tarihin Girka
Image caption Takaitaccen tarihin Girka

Tun bayan nasarar da ta samu agasar kasashen Turai a shekara ta 2004, kasar Girka ke ci gaba da fuskantar koma a baya a fagen tamola.

Abinda yasa sai a wannan karon ta samu damar kaiwa gasar cin kofin duniya karo na biyu a tarihin ta. Kasar Girka ta fuskanci kalubael akan hanyarta ta zuwa Afrika ta Kudu, inda bata samu kanta ba sai a wasan kifa daya kwalan data buga da Ukraine, inda ta lashe Ukrain din daci daya da nema.

Kasar dai na da kwararrun 'yan wasan da za su jagorance ta a Afrika ta Kudu, wadanda suka hada da Georgios karagunes da Angelos Charisteas.

Gasar ta bana dai itace ta farko ga kociyan kasar Otto Rahhagel, kuma za su kara ne a rukunin B da kasashen Najeriya da Argentina da Koriya ta Kudu.

Masu sharhi na ganin ita kebin Argentina a rukunin, in ana maganar wadanda za su kai labari.