Avram Grant ne sabon kocin West Ham

Avram Grant
Image caption Sabon kocin West Ham Avram Grant, nada jan aiki

West ham United ta nada tsohon kociyan Portsmouth Avram Grant a matsayin wanda zai jagoranci kungiyar.

Kociyan wanda haifaffen Isra'ila ne, an dade ana danganta shi da kungiyar ta West Ham, tun bayanda aka kori Gianfranco Zola.

Sabon kociyan ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru hudu.

Wata sanarwa da aka fitar a shafin yanar gizo na West Ham, tace klub din yayi farin ciki da daukar sabon kociyan da yayi.

West Ham dai ta sha da kyar a kakar wasanni ta bana, sakamakon rashin nasarar da ta yi ta fama da shi.